Babbar magana: Wani Liman ya ce zinace-zinace da matarsa ke yi yana bakanta masa rai, ya nemi Kotu ta raba aurensu na shekara 20


Wani Malamin addini mai suna Alhaji Lukman Shittu, ya rokin wata Kotu mai daraja ta A da ke zamanta a Mapo a birnin Ibadan, ta raba aurensa da matarsa saboda rayuwar zina da matarsa ke yi yana bakanta masa rai. Shafin isyaku.com ya samo.

Mamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa Malam Shittu ya gaya wa Kotu cewa ya auri matarsa Fisayo shekara 20 da suka gabata, sai dai yanzu kam baya kaunarta.

Ya yi zargin cewa matarsa ta sayo sabuwar mota, ta yi masa karya cewa yan uwanta ne suka bata motar. Ya ce bincike da ya yi ya nuna cewa karya ta yi masa saboda Kwartonta ne ya siya mata motar. Mutumin da Malam Shittu yq yi zargin cewa yana halartar Masallaci da yake jagoranta.

Sai dai matarsa mai suna Fisayo ta gaya wa Kotu cewa mijinta Shittu yana zuwa gida da mata barkatai kuma mutumin banza ne da baya kula da iyalinsa.

Daga karshe Kotu ta raba auren ma'auratan bisa hurumin rashin kaunar juna. Kotu ta mika 'ya'yansu ga Fisayo kuma ta umarci Shittu ya dinga biyan Fisayo N30k kowane wata saboda kula da yaran, Kuma kada Fisayo ta hana Shittu ganin yayansa a duk lokacin da ya bukaci haka.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN