FG za ta kakaba wa BBC da DailyTrust TV takunkumi kan gudanar da shirye-shiryen bidiyo da ke " daukaka 'yan ta'adda"


Gwamnatin tarayya ta ce za a saka wa gidajen rediyon Birtaniya (BBC) da Daily trust takunkumi kan wasu shirye-shiryensu da suka daukaka ayyukan ta’addanci da ‘yan fashi a Najeriya. Shafin isyaku.com ya samo
.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammad ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Alhamis, 28 ga watan Yuli.

“Akwai wata hukuma mai kula da yada labarai wacce ita ce Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Najeriya (NBC) kuma suna sane da wadannan abubuwa guda biyu. 

Suna kallon wane bangare ne na Ka'idar Watsa Labarai da BBC da Trust TV suka karya. Kafofin watsa labarai ita ce iskar oxygen da 'yan ta'adda da 'yan fashi ke amfani da su wajen shaka.

A lokacin da wasu dandali masu daraja irin su BBC za su iya ba wa 'yan ta'adda dandalinsu suna nuna fuskokinsu kamar su taurarin Nollywood ne, abin takaici ne. Ina so in tabbatar musu da cewa ba za su yi nasara ba, za a sanya takunkumin da ya dace ga BBC da kuma Gidan Talabijin na Trust.” Inji Mohammed.

Ministan ya ci gaba da cewa, kasancewar BBC kafar yada labarai ce ta kasashen waje ba ta karkashin ka’idojin NBC ba, duk da haka, za a sanya wa kafafen yada labarai takunkumi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN