Type Here to Get Search Results !

Da duminsa: Wani bakanike ya kashe kansa haka kawai


Wani matashi dan shekara 21 mai suna Sunday Orime, ana zargin ya kashe kansa a gidansa da ke unguwar Mile 3 Diobu a Fatakwal a jihar Ribas.

Shafin isyaku.com ya tattaro cewa marigayin, makanikin koyon aikin gyaran mota ne, ya kashe kansa ne a daren Alhamis, 21 ga watan Yuli, 2022. 

Babban jami’in tsaro na al’ummar Nkpolu Oroworukwo da ke Fatakwal, Kwamared Godstime Ihunwo, wanda ya tabbatar wa Daily trust faruwar lamarin, ya ce da misalin karfe 8 na dare ne aka yi masa waya dangane da lamarin.

Ihunwo ya ce da jin lamarin, sai ya garzaya zuwa harabar gidan kafin ya tuntubi ‘yan sanda.

Ya ce an ajiye gawar Orime a dakin ajiyar gawa.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies