Ana zargin Jami’an tsaro na shiyyar Kudu maso Gabas, Ebubeagu, sun kashe baki bakwai da suka je daurin aure a garin Awomama da ke karamar hukumar Oru ta Yamma a jihar Imo. Shafin isyaku.com ya samo.
Kamar yadda DailyTrust ta ruwaito, wadanda suka halarci daurin auren suna komawa kauyensu dake garin Otulu a karamar hukumar Oru ta Gabas a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, inda jami'an tsaron suka bude musu wuta kuma suka kashe bakwai daga cikinsu.
Shugaban al’ummar Otulu, Nnamdi Agbor, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce mutane bakwai ne suka mutu nan take yayin da wasu suka bace.
“A lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa gida jami’an Ebubeagu sun gan su a kan babura suka bude musu wuta. Kamar yadda nake magana da ku, mun gano gawarwaki bakwai na mutanenmu.
Ya ce biyar sun bace, yayin da biyu kuma suka samu munanan raunuka.” Inji shi
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin