Sarkin Yandoto dake jihar Zamfara, Alhaji Garba Marafa, ya baiwa wani kasurgumin dan fashi da makami mai suna Adamu Alero sarautar gargajiya ta Sarkin Fulani Yandoto. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.
A cewar rahoton Nigerian Tribune, an gudanar da bikin nadin rawani ne a ranar Asabar, 16 ga Yuli, 2022.
An haifi Alero a kauyen Yankuzo dake karkashin karamar hukumar Tsafe amma ya girma a babban gari.
Dan shekaru 45 yana jagorantar gungun ‘yan ta’addan da ke kai hare-hare a kauyukan Tsafe da Gusau (a Zamfara) da Faskari da Kankara a Jihar Katsina.
Matakin na ba sarkin ‘yan fashin mukami ya ta’allaka ne a kan muhimmiyar rawar da ya taka a wani shirin zaman lafiya na baya-bayan nan da aka shirya tsakanin masarautu da ‘yan bindigar da ke addabar karamar hukumar Tsafe.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa jaridar cewa; "Aleru ya kasance kan gaba a kokarin samar da zaman lafiya na baya-bayan nan a masarautun Yandoto da Tsafe."
Majiyar Sunday Tribune ta kuma bayyana cewa kwanan nan masu ruwa da tsaki da dattawa sun gana da shugaban ‘yan fashin domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
“A karshen taron, shi (Aleru) ya amince da a daina kai hare-hare kan al’ummomi da kauyukan masarautar, ya kuma amince mutane su yi noma,” inji majiyar.