Siyasar Kebbi: Jigon matasa a jihar Kebbi Ibrahim Dan Kubura ya fice daga jam'iyar APC ya koma PDP, ya yayyaga katin zama APC


Fitaccen matashin Malami Ibrahim Dan Kubura wanda aka fi sani da Imamu Junior, ya fice daga jam'iyar APC zuwa jam'iyar PDP a jihar Kebbi.

Shafin isyaku.com ya samo cewa Imamu ya fice daga jam'iyar APC tare da dimbin magoya bayansa bayan ya yayyaga katin zama dan APC kuma ya yanki katin zama dan jam'iyar PDP.

Imamu ya shaida wa kafar labarai na yanar gizo isyaku.com cewa 

" Na fice daga jam'iyar APC zuwa PDP ne saboda rashin adalci da rashin mutunta al'umma"

Yanzu dai ta tabbata cewa cewa jam'iyar APC na fama da manyan matsalolin cikin gida a jihar Kebbi, duba da wani faifen bidiyo da wani jigo a jam'iyar ya fitar a shafukan Facebook dangane da matsalolin da ake zargin sun faru a lokacin jigilar Alhazan jihar Kebbi zuwa kasar Saudiya, da kuma tarin wasu korafe-korafe na rashin gamsuwa da tsari da ke zagayawa tsakanin yan jam'iyar a jihar Kebbi. 

Kazalika jita-jita mai karfi na yawatawa a tsakanin al'ummar jihar Kebbi kan sahihancin daurewar jam'iyar APC matsayin tsintsiya madaurinki daya kafin zabukan 2023. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN