Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu biyo bayan nassarar dan takarar jam’iyyar PDP Sanata Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar. Shafin isyaku.com ya samo legit.ng ta ruwaito.
Oyetola ya ce ya amince da sakamakon zaben Gwamna da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, inji rahoton jaridar The Nation.
Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Oyetola, Ismail Omipidan ya fitar, ta ce jam’iyyar za ta mayar da martani yadda ya kamata bayan nazarin sakamakon da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, su kuma al’ummar Jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da wata matsala ba.
Gwamnan ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar da bin doka da oda. Ya kuma umurci jami’an tsaro da su dauki kwararan matakai domin hana tabarbarewar doka da oda.
A halin da ake ciki dai ana zaman makoki ne ga al’ummar Iragbiji a jihar Osun saboda dan su Gboyega Oyetola ya sha kaye a zaben Gwamnan jihar ta Kudu maso Yamma a karo na biyu.
Da sanyin safiyar Lahadi, 17 ga watan Yuli, hotunan da wakilin Legit.ng ya dauka sun nuna yadda garin ke cikin kwanciyar hankali.
Duk da cewa ’yan kabilar Iragbiji da sauran jama’ar karamar hukumar Boripe sun ba Oyetola kuri’u 21,205, bai isa ya zama Gwamnan Osun a karo na biyu ba.
Adeleke ya ya magantu bayan ya doke Oyetola a zaben gwamnan Osun
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Adeleke ya mayar da martani ga nasarar da ya samu a zaben gwamna na 2022 a jihar Osun.
Jim kadan bayan da INEC ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben, Adeleke ya yi amfani da tabbataccen shafinsa na Twitter inda ya aika sako ga mabiyansa da sauran 'yan Najeriya a dandalin sada zumunta.
"Na kawo haske a jihar Osun," ya wallafa a shafinsa na Twitter.