Ministan Sharia Kuma Antoni Janar na Najeriya Abubakar Malami SAN ya bayyana alhini da kidimewa bayan samun Labarin rasuwar abokansa guda uku a mumunar hatsarin mota.
Malami ya wallafa wani takaitaccen jawabin ta'aziyya a shafinsa na Facebook bayan samun Labarin rasuwar mutanen.
Ya ruwaito cewa:
"Labarin yana da ban tausayi da ban tsoro. Na firgita kuma na dimauce .
Nayi asarar abokai na tun kuruciyar mu na yaranta guda 3 a lokaci daya. Pharmacist Hussaini Abdullahi (Goro) Hon. Aliyu Tanko (Kwara) da Abubakar Abdullahi (Tsoho) da wani mutum daya. Mummunan hatsarin mota ya rutsa da su a hanyar su ta zuwa Birnin kebbi daga Abuja ba tare da sanin taron da muka yi da karfe 10 na safe na ranar 7 ga watan Yuli ke gudana a ranakun karshe na rayuwansu a doron kasa ba ne.
Inna lillhi wa Inna ilaihi rajuu
Allah ya jikan su da rahama.
ABUBAKAR MALAMI, SAN"
Rubuta ra ayin ka