Yan sanda a Uganda sun kama wata mata mai suna Tilutya Suzan da laifin kashe ‘yarta ‘yar shekara 7 mai suna Namugaya Mercy. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.
An tsinci gawar yarinyar da ba ta da rai a cikin gonakin rake a kauyen Nkalenge da ke karamar hukumar Busede a gundumar Jinja a ranar Alhamis, 7 ga watan Yuli.
A cewar kafofin yada labaran kasar, mahaifiyar mai shekaru 35 ta shake diyarta har lahira tare da jefar da gawarta a gonar.
Rundunar ‘yan sandan Kakira ta cafke Tilutya domin ci gaba da bincike.