Abubakar Malami ya aike sako na musamman ga jama'ar Najeriya, duba ka gani


Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a Dr. Abubakar Malami, SAN yana taya al’ummar Musulmin Jihar Kebbi da ma sauran al’ummar Musulmi murnar zagayowar bukukuwan Babbar Sallah na bana. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

AGF Malami ya ce Eidul Adha yana tunatar da Musulmi da su kasance masu biyayya da zuciya daya ga umarni da dokokin Allah Madaukakin Sarki kamar yadda Annabi Ibrahim, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi.

Malami ya ce:

“Yayin da muke gudanar da wannan gagarumin biki, ya kamata mu yi tunani a kan darussa na asali na hakuri, sadaukarwa da mika wuya ga yardar Allah da Annabi Ibrahim ya nuna a lokacin da Allah ya umarce shi da ya yanka dansa tilo (Isma’ila), ta hanyar sadaukar da kanmu ga kara riko da Dokokin Ubangiji da kuma nuna hakikanin ruhin Musulunci a cikin dukkan ayyukanmu".

 "Yayin da muke bikin Eidul Adha, dole ne mu yi la'akari da duk abubuwan da ke faruwa a kasarmu, domin mu yi amfani da lokacin yin addu'a don Allah ya kawo mana dauki ga matsalolin tsaro da tattalin arziki da ke addabar kasar nan wanda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke ciki. Malami ya kara da cewa.

Ministan ya kuma yi kira ga ’yan uwa maza da mata na kasa mai tsarki da suke gudanar da aikin Hajjin bana da su yi ta addu’ar nema wa Najeriya zaman lafiya.

“Ina son na sake tabbatar muku cewa Gwamnatin Buhari za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen ganin an tabbatar da zaman lafiya a kasar nan, ina rokon Allah Ya karbi addu’o’inmu na ganin an samu dawwamammen zaman lafiya a jihar Kebbi da kasa baki daya tare da samar da zaman lafiya a siyasance, mika mulki farkon shekara mai zuwa" Inji Malami. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN