Zaben fidda gwanin APC a Kano: An kaddamar da bincike kan kisan mutane 3

 


Hukumar kare hakkin dan adam ta kasa (NHRC), tare da hadin gwiwar kungiyar KCSF, sun kaddamar da wani kwamitin domin bincike cikin lamarin kisan mutane uku yayin zaben fidda dan takarar gwamnan jam’iyyar Progressives Congress (APC) a jihar Kano.

Daily Trust ta rahoto cewa wani dan takarar gwamnna a jam’iyyar, Sha’aban Sharada, ya yi zargin cewa an kashe magoya bayansa yayin da aka jikkata wasu a yayin zaben wanda ya gudana a ranar Alhamis da ta gabata.

Kungiyoyin sun yi zargin cewa jami’an gwamnati sun ci zarafin mutane da kuma hana deleget din Sharada kada kuri’a a zaben.

Idan za a tuna, mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna ne ya lashe zaben fidda gwanin.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN