Yadda artabu tsakanin Mafarauta da yan Boko Haram ya yi sanadin kashe rikakken Kwamandan Boko Haram a Borno

 


Mohammed Yohanna, shugaban kungiyan mafarauta da yan vigilante na yankin arewa maso gabas ya ce mambobin tawagarsa sun kashe wani kwamandan Boko Haram da mataimakinsa a Borno, rahoton The Cable.

Yohanna, wanda ya bayyana hakan a hira da aka yi da shi a ranar Talata da manema labarai, ya ce an yi artabu tsakanin yan ta'adda da mafarauta a kauyen Shaffa Taku da ke karamar hukumar Damboa a Borno a ranar Litinin, Vanguard ta rahoto.

Mafarautan sun kwatto AK-47 da babur guda daya

Ya kara da cewa an kwato babur da kuma bindiga AK-47 daga hannun yan ta'addan.

Mun samu bayyanai na sirri daga wurin wasu da suka fada mana yan ta'addan na adamar garuruwansu makonni biyu da suka gabata," in ji shi.

"Bayan samun bayanan, na tattara tawaga ta kuma muka dira wurin da yamma a Shaffa Taku, wani gari da mutane suka tsere daga cikinsu a Damboa.

"Mun yi sa'a, muka hangi yan ta'addan kimanin su 20, kan babura. Muka yi musayar wuta da su kuma muka kashe kwamandansu da mataimakinsa, yayin da saura suka tsere da rauni.

"Mun kuma kwato babur daya da AK-47 guda daga hannun yan ta'addan. Na sanar da jami'an tsaro na bataliya 231 a Biu, kuma za mu hadu a yau domin mika musu AK-47 din da babur."

Yohanna ya kuma ce a halin yanzu mafarautan sun kama wasu mtane da ae zargin suna kai wa yan ta'addan kayan abinci.

A cewarsa, an kama wadanda ake zargin da kudi Naira miliyan 6.05 a wani kauye a karamar hukumar Hawul.

Ya ce an mika mutanen da aka kama ga jami'an tsaro domin daukan mataki na gaba.

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.

A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.

Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN