Yarjejeniya: Buhari zai zaba daga cikin masu neman zaben shugaban kasa bayan Gwamnonin APC sun gabatar da jerin sunayen mutum hudu na musamman


A daidai lokacin da shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya zama dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2023, Gwamnonin da ke karkashin jam’iyyar sun dauki wani mataki mai tsauri. 

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito , Gwamnonin jam’iyyar APC, domin tabbatar da adalci wajen zaben fidda gwani, sun fitar da jerin sunayen ‘yan takarar da ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zaba. 

An tattaro cewa jerin sunayen ya ba da amsa mai kyau ga kiran da ake yi a fadin kasar na a mayar da mulki zuwa kudanci kuma saboda haka yana da karin ‘yan takara daga yankin. 

Majiyar ta ruwaito tana cewa:

 "Sun zabi daya daga kudu maso gabas, daya daga kudu maso kudu, uku kuma daga shiyyar kudu maso yamma kamar yadda suke cewa mulki ya koma kudu."

 Jerin, wanda kuma Nigerian Tribune ta gani, yana da sunaye kamar haka:

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo 

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Gwamna Kayode Fayemi 

Rotimi Amaechi 

Gwamna Dave Umahi 

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE