Zaɓen magajin Buhari a APC: Duba abin da ke faruwa da yan Jarida a wajen taron


Yan jaridun da aka tura domin su ɗakko abubuwan da ke faruwa a babban taron APC na ƙasa da ke gudana a Filin Eagle Square Abuja sun gaza samun damar shiga.

Daily Trust ta tattaro cewa hakan ta faru ne bisa gazawar kwamitin jam'iyyar APC na ɓangaren midiya karkashin gwamna Abdullahi Sule. Har yanzu kwamitin bai raba wa yan jaridun katin shaida ba 'Tags'.

A wata sanarwa da jam'iyyar APC ta fitar dangane da taron, za'a fara aiwatar da abun da ya tara mutane wurin da misalin ƙarfe 10:00 na safe, farawa da isowar Deleget.

Tun mako biyu kafin wannan rana, Gidajen jaridu waɗan sa suka shirya ma'aikatan da zasu ɗakko musu rahoton abin da ke faruwa, sun rubuta takardan neman izinin APC.

Rahotanni sun ƙara da bayyana cewa hatta masu tattara rahotannin jam'iyyar APC na babbar Sakatariya ta Abuja na nan na jiran a ba su nasu katunan don shiga wurin.

Yan jaridun da suka isa Filin Eagle Square tun da sanyin safiyar Talata, suna nan zaune suna cigaba da jiran sahalewar jam'iyya domin jami'an tsaron da aka girke a wurin sun hana su shiga.

Wani ma'aikaci ya kai karar jaruma Hadiza Gabon gaban Kotun Shari'ar Musulunci kan ta karya masa alƙawarin aure.

Bala Musa ya shaida wa Kotun sun jima suna soyayya da Gabon kuma ta masa alƙawarin aure, shiyasa da ta nemi Kuɗi yake tura mata.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN