Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC ta dare gida biyu bayan sanar da Lawan a matsayin ɗan takara


Mambobin kwamitin gudanarwa NWC na jam'iyyar APC ta ƙasa sun rabu gida-gida kan zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na maslaha.

Punch ta rahoto cewa mambobin NWC sun gana ranar Talata domin biyayya ga umarnin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na cewa ya kamata a zaɓi magajinsa ta hanyar sulhu.

Rahotanni sun bayyana cewa yayin taron, an sanar da wani ɗan takara da sunan shi ne zaɓin shugaba Buhari, amma mambobin NWC suka yi watsi da shi nan take.

Wani mamba a kwamitin NWC ya shaida wa wakilin jaridar cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, aka sanar musu da sunan ɗan takarar maslaha.

Hakan ya sa wasu mambobin kwamitin NWC suka yi watsi da lamarin sakamakon haka aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin su.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN