Yanzu-yanzu: Matasa sun kashe wani Musulmi kan zagin Manzon Allah (SAW) a Abuja


Wasu matasa a ranar Asabar sun hallaka wani dan kungiyar Bijilante kan zargin kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW) a birnin tarayya Abuja.

An tattaro cewa an hallaka dan Bijilantin ne a sashen yan Timba dake kasuwar kayan itace a unguwar FHA Lugbe, rahoton Punch.

Wani mai idon shaida yace dan Bijilantin Musulmi ne kuma ya shahara da zagin manzon Allah amma yayi wani sabo da daren jiya.

A riwayar Daily Trust, bayan kalaman batancin, sai ya gudu ya nemi mafaka a Ofishin yan Bijilanti dake kasuwar misalin karfe 1 na rana.

An tattaro cewa a wannan lokacin fusatattun matasa suka kure masa gudu suka fito da shi karfi da yaji daga cikin ofishin kuma suka kasheshi kai tsaye, daga baya suka konashi.

Wani dan kasuwa a wajen mai suna Halilu yace:

"Sunan mutumin Small Hundaru, wannan ba shine karon farko da zai zagi annabi ba."

"An damkeshi yana kokarin sayen abinci a kasuwa da rana, saboda lokacin da yayi batancin, babu mutane sosai a wajen, sai aka buga masa ice a akai. Sai da aka kwace bindigar hannunsa suka lallasa shi."

"Daga baya suka masa jifa kafin ya gudu ofis. Abokan aikinsa sun gaza kareshi saboda adadin mutanen da suka kure masa gudu. Da ya sume suka zuba masa fetur suka banka masa wuta a gaban ofishinsu."

Rahoton ya kara cewa yan sanda sun harbi mutum uku cikin matasan.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN