Cikakken farashi: Alhazai zasu biya kasa da N2.5m a Hajjin bana


Alhazan da suka tashi daga yankin kudancin Najeriya na shekarar 2022 za su biya Naira miliyan 2,496,815.29, yayin da wadanda suka tashi daga yankin arewacin Najeriya za su biya N2,449, 607.89.

Wadanda suka tashi daga Adamawa da Borno za su biya N2,408,197.89 saboda kusancin su da Saudiyya.

Mahajjata masu niyya kuma za su yi gwajin COVID-19 PCR akan rangwamen kudi na N30,000.

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da farashin kudaden a ranar Asabar a Abuja, ta kuma ce farashin kudin jirgi ya danganta da nisan Maniyyata. 

Shugaban hukumar kuma babban jami’in hukumar Alhaji Zikrullah Hassan a wata sanarwa da ya fitar ya ce hukumar ta bukaci a kara yawan maniyyata daga Najeriya kuma tana jiran amsa daga Saudiyya.

Ya kuma umarci hukumar jin dadin alhazai a matakin jihohi da su ci gaba da gudanar da aikin hajjin da aka ware musu maimakon jira a kara musu kaso.

Ya bayyana cewa, a yayin da ake shirin bizar jami’ai da mahajjata a cikin jirgin na farko, ya kamata jihohi su fara sarrafa bizar ga dukkan nau’o’in maniyyatan da suka yi rajista.

Hassan ya kuma bayyana cewa hukumar shige da fice ta Najeriya ta yi alkawarin taimakawa jihohin da ke fama da matsalar sarrafa fasfo na balaguro ga maniyyata.

Hukumar NAHCON ta bukaci jihohi da su gaggauta kammala kudaden da ake turawa alhazai domin gudanar da shirye-shirye cikin gaggawa da kuma sarrafa manyan kudaden alawus na balaguro ga maniyyata.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN