Yan ta'adda sun kai farmaki sansanin Sojoji a Borno, sun yi awon gaba da makamai


Wasu 'yan bindiga da ake zargin mayakan ISWAP ne, sun kai wa sansanin sojoji farmaki a daren Laraba a jihar Borno.

Daily Trust ta gano yadda hatsabiban suka kai wa dakarun hari a kauyen Ajire cikin karamar hukumar Mafa misalin karfe 9:00 na dare, wanda hakan ya tilasta sojin ranta a na kare ba tare da wata kwakwkwarar musayar wuta ba

Majiya ta bayyana yadda kimanin soji 80 a sansanin suka tsere, tare da barin wasu makamai da kayayyakin da suka hada da wayoyi, wanda hatsabiban suka yi awon gaba dasu.

An ruwaito yadda sojojin suka gaza yin fito na fito da 'yan bindigan saboda rashin carbin harsasai da kayan yaki.

"'Yan ta'addan sun fattaki dakarun sojin Najeriya da aka bari da tsirarun carbin harsasai kuma ba tare da kayayyakin da za su kare kansu su irin su RPG, AA da MG," a cewar majiyar.

Mazauna yankin sun bayyana yadda 'yan ta'addan suka kai farmaki kauyen Ajire tsakanin karfe 9:00 na dare zuwa karfe 4:00 na yammacin Alhamis, sai dai basu hari mutanen yankin ba, amma an ga yadda suke tattara muhimman abubuwa a sansanin sojojin.


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE