Buhari: "Wanda ya jarraba tazarce karo na uku bai gama lafiya ba"


Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa ba zai nemi karin wa’adi idan lokacinsa ya cika ba, ya jaddada barinsa mulki a 2023.

Da yake jawabi a wajen taron CHOGM na kasashen renon Birtaniya da ake yi a Kigiali, kasar Rwanda, Muhammadu Buhari ya ce ya gama yin takara.

Daily Trust ta rahoto Buhari a tattaunawarsa da Firayin Ministan Birtaniya, Boris Johnson yana cewa wanda ya nemi ya zarce a karo na uku bai ji dadi ba.

Boris Johnson ya tambayi shugaban Najeriyan ko zai nemi ya sake takarar shugaban kasa. A amsar, ya yi wata magana da bai ambaci sunan wani ba.

Da ya tashi bada amsa, Mai girma Muhammadu Buhari ya yi wata magana mai harshen dabo, wanda ta sa wadanda suke wurin, suka fashe da dariya.

Wanda ya jarraba bai ji dadi ba

“In nemi wani wa’adin? A’a! Wanda ya fara yunkurin hakan bai ji dadi sosai ba.” - Muhammadu Buhari.

Shari'ar Mazi Nnamdi Kanu

Jaridar ta ke cewa shugaba Buhari ya yi watsi da zargin da ake yi na cewa an hana jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu damar ganawa da lauyoyinsa.

A wani jawabi da shugaban kasar ya fitar ta hannun Femi Adesina, ya tabbatar da cewa an ba Kanu hakkinsa duk da irin cin mutuncin da ya yi wa Najeriya.

“Kanu ya yi ta fadar maganganun banza a game da Najeriya a lokacin da yake Birtaniya, a lokacin da aka kama shi, sai mu ka maka shi a kotu.”

“Sai ya kare duk abubuwan da ya fada a can. Lauyoyinsa su na haduwa da shi. Idan za a tuna, ya taba tserewa, za mu tabbata bai sake yin haka ba.”

- Femi Adesina

Har ila yau, Buhari wanda ya rage masa kasa da shekara guda ya bar mulki, ya yi bayanin irin kokarin da gwamnatinsa ta ke yi a kan matsalar rashin tsaro.

Zaben 2023

Ku na sane cewa Atiku Abubakar ya na ikirarin ya yi arziki ne tun a gidan kwastam, shi ma Bola Tinubu yana cewa kafin ya shiga siyasa ya zama Attajiri.

Amma a 1993 an taba kai Bola Tinubu kotu bisa zargin alaka da kudin harkar kwayoyi. Sannan an taba zargin Atiku Abubakar da boye $40m a kasar Amurka

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN