Dokar Zabe: Kotun Koli ta yanke hukunci a kan Buhari da karar Malami kan dokar zabe ta 2022 sashe na 84 (12) da aka yi wa kwaskwarima


An soke karar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami suka shigar na neman a soke dokar zabe ta 2022 sashe na 84 (12) da aka yi wa kwaskwarima
. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

A wani hukunci da aka yanke a ranar Juma’a, 24 ga watan Yuni, wasu Alkalai bakwai a Kotun koli karkashin jagorancin mai shari’a Musa Dattijo Mohammed, sun bayyana cewa Buhari ya sa hannu wajen samar da dokar ta hanyar amincewa da ita ba zai iya waiwaya don yin kuskuren tanade-tanaden ta ba. .

Legit.ng ta labarta cewa Alkalin kotun mai shari’a Dattijo ya kuma amince da korafe-korafen da Majalisar dokokin kasar da sauran wadanda ake tuhuma suka gabatar a kan karar.

A cewar kotun kolin, karar da shugaban kasar da AGF dinsa ke yi, wani hari ne kan tsarin dimokuradiyya da kuma cin zarafin Kotu da kuma raba madafun iko.

A hukuncin da kotun ta yanke, mai shari’a Emmanuel Agim ya ce shugaban kasa ba zai iya neman umarni ko neman Majalisar ta yi wata doka ko sauya kowace doka ba.

Kalamansa:

“Shugaban kasa ba shi da ikon umurtar Majalisar Dokoki ta kasa ta yi gyara ko aiwatar da wani aiki...ya saba wa ka’idar raba madafun iko.

"Babu wani bangare na Kundin Tsarin Mulki da ya sanya yin amfani da ikon Majalisa bisa umarnin shugaban kasa."

Malami ya bayyana abin da dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima zai haifar da karuwar rashin tsaro a Najeriya

Malami ya ce kudirin dokar zabe da shugaba Buhari ya ki sanyawa hannu zai kara tabarbarewar rashin tsaro idan an bar shi ya ci gaba da zama.

Ministan wanda ya bayyana haka ya kuma dage kan cewa kudirin dokar zabe yana da nasaba da kashe kudi da ya wuce kima.

Ku tuna cewa shugaba Buhari ya ki amincewa da kudurin dokar ne saboda zai iya kawo cikas ga dokar da ta shafi harkokin zabe.

An zana layin yaki yayin da Buhari da Malami suka kai NASS Kotun Koli

Fadar shugaban kasa da ma'aikatar shari'a ta Najeriya sun maka Majalisar dokokin kasar kara kan sashe na 84(12) na dokar zabe ta 2022.

Haɗaɗɗen Majalisar ita ce wanda ake tuhuma a cikin ƙarar da aka shigar a Kotun Koli game da sashe mai cike da cece-kuce a cikin dokar.

Shugaba Buhari da AGF Abubakar Malami suna kira ga kotun koli da ta yi watsi da wannan magana.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN