Yan sanda sun cafke mahaifi da ya yanke dansa mai shekara daya da zarto domin yin tsafi


Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta kama wani matashi mai shekaru 33 da haihuwa mai suna Gabriel Volts bisa zargin fille kan dansa domin yin tsafi. 

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, wanda ake zargin ya dauki dansa daga hannun matarsa, sannan ya tafi daji mai suna Etinabobo da ke jihar Edo inda ya yi amfani da zarto ya yanke kan yaron.

"Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta kama wani mai suna Gabriel Volts mai shekaru 33 da haihuwa wanda ake zargi da fille kan dansa domin yin tsafi. Wanda ake zargin ya yi amfani da zarto ya yanke kan dan nasa dan shekara daya da wata takwas a dajin Etinabobo da ke jihar Edo domin yin tsafi tare da binne shi kuma ya yi amfani da ganyen bishiyar dabino wajen rufe kabarin.

An kama wanda ake zargin ne bayan yaron ya bace, kuma wanda ake zargin ya yi wa matar karya cewa dan yana tare da ‘yar uwarsa a Warri, wanda hakan ya sa matar ta yi shakku, don haka ta kai rahoto ga ‘yan sanda. Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa'' cewar rahoton Kakakin Yan sandan jihar. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN