Kayya: An kama matashi ya taushe tsohuwa mai shekara 75 turmi-tabarya yana yi mata fyade a gona


Rundunar ‘yan sanda a Anambra, a ranar Asabar ta kama wani mutum mai shekaru 30. Sunday Nwadiagha, bisa zargin yi wa wata tsohuwa mai shekaru 75 fyade. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya ruwaito
.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar a ranar Asabar a Awka, ta ce tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro, an kama wanda ake zargin wanda ya fito daga yankin Eyiba a Ebonyi da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Juma’a, a unguwar Nkwelle Awkuzu.

DSP Tochukwu Ikenga jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra (PPRO) wanda ya sanya wa hannu a sanarwar, ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa an kama wanda ake zargin ne da aikata laifin a gonar wanda abin ya shafa a Nkwelle Awkuzu.

“Kamen wanda ake zargin ya biyo bayan ihu da tsohuwa ta yi, wanda ya ja hankalin masu wucewa da makwabta da suka garzaya wurin da lamarin ya faru suka kama mai laifin turmi-tabarya kan tsohuwar y taushe ta Yana jima'i da ita,” inji shi.

Ikenga ya kara da cewa kafin kama shi da mika shi ga ‘yan sanda, tuni wasu fusatattun mutane suka taru inda suka yi wa Nwadiagha dukan tsiya.

Mai laifin yana fuskantar tambayoyi a wajen Yan sanda.

SANARWA

Yadda za mu taimaka maka a fagen siyasarka ko kasuwancinka.

* Ko Ina a Duniya ana samun shafinmu na isyaku.com

* Muna da subscribers Miliyan 8

* Muna cikin group na WhatsApp guda 447

*Muna da group namu na kampaninmu na isyaku.com guda 22.

* Muna aiki ne karkashin kampani mai cikkken rijista da CAC Seniora int'l Ltd RC1470216.

* Rijistar da kowane gidan Jarida ta yi a Najeriya shi ne muka yi.

* Za mu iya tallata maka kasuwancinka ko siyasarka ta hanyar ingizon yanar gizon  zamani. 

* Kada sunan isyaku.com ya sanyaya maka guiwa a jaridance, sunan Jarida ra'ayi ne.otocin Honda, Toyota, Mitsubishi, Mercedes duk sunayen mutane ne.

LATSA NAN KA TUNTUBE MU

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN