Yan bindiga sun sace matar shugaban jam’iyyar APC na wata karamar hukuma a jihar Neja


Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta'adda ne sun yi garkuwa da matar shugaban karamar hukumar Magama na jam’iyyar APC a jihar Neja, Hon. Usman Baffa Ibeto. 

Har yanzu babu cikakken bayani game da lamarin har zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto amma an tattaro cewa an dauke Mrs Baffa daga gidanta da ke unguwar Tunga a Minna a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni. 

Rahotanni sun ce har yanzu wadanda suka dauke ta ba su tuntubi danginta ba domin neman kudin fansa.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN