Mataimakin Tinubu: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da Gwamnonin APC 7 a Villa


Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shiga taron sirri yanzu haka da gwamnonin APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban gwamnonin da suka É—are kan madafun iko a APC, Gwamna Atiku Bagudu, na jihar Kebbi, shi ne ya jagoranci takwarorinsa zuwa wurin Buhari.

Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar APC ke cigaba da faɗi tashin zakulo mataimaki ga ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Mutanen da suka halarci taron

Taron wanda ke gudana yanzun ya samu halartar shugaban ma'ikatan fadar gwamnatin tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari, da Sakataren gwamnati, Boss Mustapha.

Haka nan kuma a É—aya É“angaren gwamnonin da suka je wurin taron sune, Babagana Zulum na Borno, Nasir El-Rufai na Kaduna, Abdullahi Sule na Nasarawa, Badaru Abubakar na Jigawa.

Sauran sune, gwamna Simon Lalong na jihar Filato, Yahaya Bello na jihar Kogi da kuma gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.

Channels TV ta ruwaito cewa duk da babu cikakken bayani kan dalilin taron amma ya zo ne mako ɗaya bayan kammala zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa.

Su wa ake tsammanin zaben mataimaki daga cikin su?

Rahoto ya nuna cewa tsohon gwamnan Legas É—in ya rubuta sunan tsohon gwamna Borno, Kashim Shettima, wanda ya taka rawa wajen nasararsa a matsayin wanda ya ke son ya zama mataimaki.

Mambobin tsohuwar jam'iyyar CPC da ta cure zuwa APC, suna shirin gabatarwa Buhari da sunan Abubakar Malami da Hadi Siriki don zaɓar ɗaya ya zama mataimaki.

Tsohon sakataren gwamnati, Babagana Kingiɓe, wanda ya kasance mataimaki ga MKO Abiola a zaɓen 1993 ya tura sunayen mutum uku ga Tinubu domin duba wa.

Mutanen sun haÉ—a da gwamna Babagana Umaru Zulum, mataimakiyar shugaban majalisar É—inkin duniya, Amina J Muhammed, da kuma Kashim Ibrahim-Imam.

Yayin da manyan jam'iyyu ke ta faÉ—i tashin neman mataimaki, Farfesa Umeadi, ya kawo karshen kace-nace a jam'iyyar APGA.

Ɗan takarar da jam'iyyarsa sun amince Kwamaret Muhammed Koli ya zama mataimaki yayin zaɓen 2023.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN