Yanzu yanzu: Kotu ta sa ranar yanke wa makashin Hanifa hukunci a Kano, duba ka gani


Mai shari’a Usman Na’abba na wata babbar kotun jihar Kano ya sanya ranar 28 ga watan Yuli domin yanke hukunci kan karar kisan da aka yi wa Hanifa Abubakar ‘yar shekara biyar.

Alkalin kotun ya sanya ranar yanke hukuncin a yau 14 ga watan Yuni bayan amincewa da rubutaccen gabatarwar karshe da bangarorin suka yi.

An sace marigayiya Hanifa ne a ranar 4 ga Disamba, 2021, a kan hanyarta ta komawa gida daga makaranta, kuma daga baya aka gano cewa an kashe ta. Bayan dogon bincike, sai aka kama Tanko, kuma ya amsa laifin yin garkuwa da yarinyar tare da kashe ta da gubar bera naira 100 kafin a binne ta a wani kabari mara zurfi a daya daga cikin makarantunsa amma daga baya ya janye zancen kasheta, ya yarda ya sace ta.

An gurfanar da Abdulmalik da sauran mutane uku tare da abokin harkallarsa Hashim Isyaku da Fatima Jibril Musa a gaban wata babbar kotun jihar Kano bisa laifuka biyar da suka hada da hada baki, garkuwa da mutane, tsare mutane, da kuma kisan kai wanda ya sabawa sashi na 97, 274, 277, 221 na lambar laifi.

A zaman da aka ci gaba da sauraron karar a yau, mai shigar da kara a karkashin jagorancin Lamido Abba Soron Dinki, ya bukaci kotun da ta yi la’akari da jimillar shaidun da aka gabatar a gabanta domin samun wadanda ake tuhuma da laifukan da ake tuhumarsu da su tare da yanke musu hukuncin kisa.

“Muna kira ga kotu da ta zartar da hukuncin kisa ga duk wadanda ake tuhuma saboda hukuncin da aka yanke musu wanda ake tuhumarsu da shi yana da hukuncin kisa daya”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN