Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da yi wa wata mata mai tabin hankali fyade a karamar hukumar Song da ke jihar. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.
Kakakin rundunar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, a wata sanarwa a ranar Juma’a, 24 ga watan Yuni, ya ce an kama wadanda ake zargin, Kwallan John da Imamu Abdurrahman, a ranar Lahadin da ta gabata.
“A ranar 19/6/2022 an kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin hada baki da kuma yi wa wata ‘yar shekara 35 fyade. Matar ‘yar shekara 35 ta tana da lalurar tabin hankali a kauyen Dirma, karamar hukumar Song,” in ji PPRO.
“Wadanda ake zargin dan shekara 23 mai suna Kwallan John dan shekara 23 da Imamu Abdulrahman dan shekara 21 duk mazauna kauyen Dirma da ke karamar hukumar Song, sun hada baki suka tafi da ita wani gini da ba a kammala ba sannan suka yi lalata da ita da karfi.
“’Yan sanda sun kama wadanda ake zargin ne a hedkwatar shiyya ta Dumne, biyo bayan rahoton da aka samu daga wani dan unguwar Simon D. Adamu.”
Bincike ya zuwa yanzu ya nuna cewa wadanda ake zargin sun yi amfani da yanayin rashin lafiyarta suka vutar da ita, in ji kakakin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sikiru Akande ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin tare da fara gurfanar da wadanda ake zargin a gaban Kotu.