Jama'ar gari sun aika wani 'kidnapa' barzahu da gaggawa suka kone gawarsa, duba abin da ya faru


Wasu fusatattun mutane sun kona wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuni a garin Obosi da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra.

Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya ruwaito cewa shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne lokacin da tawagar matasan Obosi da jami’an tsaro suka tare ‘yan ta’addan inda suka bukaci da a binciki Motar da suke ciki. , an same wasu ma'aurata miji da matarsa da aka sato aka sa a cikin motar kuma an ceto su nan take.

An ce wadanda ake zargin sun yi garkuwa da mutanen ne suka bude wuta a kan jama’ar, inda jama'a suka amsa musu da “wuta ga wuta” aka yi jarbe-harbe da bindigogi har sai da aka ci karfinsu. An harbe daya daga cikin masu garkuwa da mutane a yayin da ake musayar wuta tare da kona gawarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya kuma tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an kubutar da ma’auratan da aka yi garkuwa da su, sannan an kwato motoci biyu kirar Toyota Highlander jeep mai lamba NSH 398 HA da Toyota Camry mai lamba BRS 941 AA daga hannun wadanda ake zargin. masu garkuwa da mutane.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN