Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) Rabi'u Kwankwaso ya kai wata ziyarar sirri ga gwamnan Rivers, Nyesom Wike a ranar Juma'a, 24 ga watan Yuni. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.
Legit.ng ta ruwaito cewa Kwankwaso, wanda ya jagoranci tawagar shugabannin jam’iyyarsa da abokansa, an ce ya yi wata tattaunawa mai ma’ana da Wike a bayan fage.
Kwankwaso, bayan taron wanda tsohon Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya halarta, ya dauki hotuna da yamma, ba tare da bayyana dalilin ziyarar tasa ba, inji rahoton jaridar The Nation.
Sai dai an samu labarin cewa tsohon Gwamnan na Kano a taron da aka gudanar a ranar Juma’a a gidan Gwamnan Jihar jihar Riverd da ke Birnin Fatakwal ya nemi goyon bayan Wike kan kudirinsa na Shugaban kasa.
Kwankwaso ya zo ne kwanaki kadan bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP) Peter Obi ya kai irin wannan ziyarar ta sirri ga Wike.