Yadda wani kato ya yi shigar mata ya kutsa dakin kwana na dalibai mata a wani kwalejin arewa, duba abin da ya faru


Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wani matashi dan shekara 25 bisa zarginsa da aikata laifuka da kuma yunkurin yin sata.

An kama Jika John, wanda dan karamar hukumar Michika ne, amma yana zaune a Sabon Pegi a Wuro Chekke, karamar hukumar Yola ta Kudu, a jihar Adamawa, a ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, 2022.

Rahotanni sun bayyana cewa ya yi shigar mata sannan ya shiga Kwalejin koyon aikin jinya da unguwar zoma ta Yola inda ya saci silinda mai iskar gas a dakin kwanan dalibai mata.

An kama shi ne biyo bayan kiran gaggawa da Kwalejin ta yi wa Yan sanda.

Da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar ‘yan sandan, wanda ake zargin Jika ya yi ikirarin cewa akwai wata yarinya a makarantar da ta nemi ya kawo mata ziyara domin yin lalata da ita.

Wanda ake zargin ya ce ya shirya da yarinyar ne a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni, 2022, domin su hadu a ranar Litinin da duk abokan zamanta za su fita daga hostel.

Ranar litinin tazo sai ya saka kayan mata don samun saukin shiga hostel.

Jika ya ce jami’an tsaro sun kama shi a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa hostel da misalin karfe 7:30 zuwa 8:00 na dare.

Ya dage cewa shirin shi ne ya je ya yi iskanci ba sata ba.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, OC Crack Squad na rundunar ‘yan sandan, CSP Ahmed Danjuma Gombi, ya ce ba gaskiya ba ne cewa yana makarantar ne ya yi lalata da wata mace, sai dai ya saci tukunyar gas ne domin ya sayar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN