Birnin kebbi: An fara shari'ar mutumin da ake zargi da kashe matar aure da diyarta a unguwar Labana a babbar Kotun jihar Kebbi


Rahotanni daga babban Kotun jihar Kebbi na cewa an gurfanar da Idris Suleiman a gaban Kotu, bisa tuhumar kisan Sadiya Idris tare da diyarta a Unguwar Labana a garin Birnin kebbi
.

An tarar da gawar Sadiya tare da diyarta ranar 11 ga watan Aprilu bayan an sareta a wurare da dama kuma aka kashe diyarta duk a gidan mijinta da ke Unguwar Labana shiyar tagwayen titin Sani Abaca da ke Birnin kebbi.

Idris tare da rakiyar jami'an kula da gidajen gyara hali sun kawo shi gaban Kotu sanye da farar Kaftani shedda kuma babu hula a kansa.

Bayan sauraron shaidu, Kotu ta dage shari'ar har ranar Laraba 15 ga watan Yuni 2022 domin ci gaba da shari'ar. 

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE