Babbar magana: Yadda Aisha Buhari ta fice daga taron APC a fusace, ta ki raka Buhari mika wa Tinubu Tuta


Rahotanni daga filin wasa na Eagle Square da ke Abuja inda aka yi zaben fidda gwani na jam'iyyar APC, sun sanar da yadda Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa ta fice daga taron cikin matsanancin fushi.

Aminiya ta ruwaito cewa, Aisha Buhari ta figi motar ta inda ta yi ficewarta daga taron ranta bace, duk da kuwa an yi taron an tashi lami lafiya.

Aminiya tattaro yadda aka dinga kiran Aisha Buhari ta raka shugaban kasa Muhammadu Buhari kan mimbari amma ta yi biris.

Wannan lamarin ya faru ne bayan tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigon jam'iyyar APC na kasa ya kammala jawabin godiya bayan nasarar lashe zaben fidda gwanin da ya yi.

An yi kiran shugaban kasa Muhammadu Buhari kan mimbarin inda ya mika tutar jam'iyya ga Bola Tinubu a matsayin wanda zai nemi kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar a 2023.

Daga cikin wadanda suka raka Buhari zuwa kan mimbarin akwai, Sanata Abdullahi Adamu, Farfesa Yemi Osinbajo da Ahmad Lawan.

Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba a san musababin fushin uwargidan shugaban kasan ba a wurin taron.

Babban mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta, Buhari Sallau, shi ne ya bayyana wannan cigaban tare da Hotuna a shafinsa na Twitter.

Shugaban tare da shugaban jam'iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, da matar Osinbajo, ya damƙa tutar yayin rufe babban taron APC wanda ya tabbatar da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban kasa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN