Yadda mahaifi mai shekara 40 ya taushe diyarsa yar shekara 13 ya yi lalata da ita da karfin tuwo, duba abin da ya biyo baya


Wata Kotun Iyali da ke zamanta a Iyaganku a Ibadan, a ranar Litinin, ta bayar da umarnin tsare wani magidanci mai shekaru 40, Abideen Akinbola, a gidan gyaran hali na Agodi bisa zarginsa da yin lalata da diyarsa. Kafar labarai na isyaku.com ya samo.

Alkalin kotun, Mista SH Adebisi, ya bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali na Agodi bisa zargin lalata da ‘yarsa ‘yar shekara 13.

Adebisi ya ce wanda ake kara zai ci gaba da zama a cibiyar gyara, har zuwa lokacin da hukumar kula da kararrakin jama’a (DPP) ta ba da shawara kan shari'arsa.

Bayan haka, ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 11 ga watan Yuli.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa, an gurfanar da Akinbola, da ke kauyen Alaje, kusa da Akanran a karamar hukumar Ona-Ara a jihar, bisa tuhumar da ake masa na yin lalata da diyarsa ta hanyar yi mata fyade.

Lauyan masu shigar da kara, Insp Gbemisola Adedeji, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara a tsakanin watan Janairu zuwa Mayu, a kauyen Alaje da ke kusa da Akanran, ya yi lalata da diyar sa ba tare da izininta ba.

Adedeji ya ce laifin ya ci karo da sashe na 34 na dokar kare hakkin yara ta jihar Oyo na shekarar 2006.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN