An kama wata matar aure da ta dauki hayar wani mutum ya kashe mijinta a Yola.
Matar mai suna Hauwa Audu ‘yar karamar hukumar Michika ce ta dauki hayar wani Kwaji Tizhe a kan kudi naira 100,000 domin ya kashe mijinta mai suna James Tizhe sannan ta fara bashi soma tabin kudi naira 7,000 .
Misis Audu a halin yanzu yana tsare a gidan yari a Yola, bisa zargin yunkurin kisan kai, an gurfanar da ita a gaban babbar kotun Majistare ta daya, saboda "yunkurin aikata kisan kai," in ji Leadership.
A cewar mai gabatar da kara, ASP Francis Audu, wadda ake zargin ta shirya makarkashiyar kawar da mijinta, James Tizhe da wasu mutane biyu da suka hada da Maryamu Bugi da Bugi Walla.
Mai gabatar da kara ya gaya wa kotun cewa wadda ake zargin ta baiwa wanda ake zargin kudi naira 7,000 daga cikin kudi N100,000 da ta yi alkawarin biya bayan ya kashe wadanda ta rubuta.
Wanda ta yo hayar ya karbi kudin soma tabin ne a ranar 3 ga Yuni, 2022, kuma ya kai karar kansa ga ‘yan sanda.
An tattaro cewa Hauwa ta biya kudin ne ga Kwaji, domin ya tuntubi wani Boka a madadinta domin ya sako masa cutar shanyewar bangare jiki ga mijinta, amma ba don ta kashe shi ba.
Rahotanni sun bayyana cewa ta dauki matakin ne saboda gazawar mijin na daukarta a matsayin matarsa da kuma kula da ita yadda ya kamata. An yi zargin cewa mijin bai hada gado daya da ita ba tsawon shekaru tara da suka wuce.
An ce wacce ake zargin ta zargi Maryamu Bugi da Bugi Walla da laifin kashe diyarta ta hanyar tsafe-tsafe a sakamakon haka ta yanke shawarar daukar fansa.
Da aka gurfanar da ita a gaban kotu, wadda ake zargin ta musanta zargin, kuma ta musanta aikata laifin. Bayan an shigar da karar ne sai mai gabatar da kara ya nemi da a dage shari’ar don ba shi damar kwafin karar sannan ya aika da ita zuwa ga DPP domin tantancewa bisa la’akari da irin laifin da ake zarginta da shi.
A hukuncin da ya yanke, Alkalin Kotun Mai shari’a Mohammed Buba, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara daga bisani ya dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga Yuli, 2022.