Wani fusataccen Makiyayi ya caka wa Direban motar Bas da yaron mota wuka har Lahira bayan ya buge ya kashe Shanunsa biyu a Legas


Rahotanni sun bayyana cewa wani da ake zargin Makiyayi ne ya daba wa wani direban motar bas ‘yar kasuwa wuka da kwandastansa bayan ya buge shanunsa guda biyu da mota suka mutu a Legas ranar Litinin. Sahara reporters ta ruwaito.

An tattaro cewa motar ta kwace wa direban me bisa ga alamu ya rasa yadda zai yi, lamarin da ya sa motar sa ta buge tare da kashe shanu biyu mallakin wanda ake zargin makiyayi ne a Agogo Igbala kusa da Mowo.

Wani mai amfani da Twitter, @ Austynzogs ne ya bayyana hakan , wanda shi ma ya saka hotuna a shafinsa na Twitter.

Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “12h35: Rikicin jama’a a Agogo Igbala kusa da Mowo, kan titin Legas/Badagry, bayan wani direba ya rasa yadda zai yi kuma ya yi amfani da motar sa ta buge tare da kashe wasu shanu biyu mallakar wani makiyayi. Makiyayin da ya fusata ya caka wa direban da kwandastan wuka har lahira.”

Hotunan da mai amfani da shafin Twitter ya wallafa ya nuna yadda mutane suka taru a kan gawar direban da shanun. Mutum na biyu da ake zargin an kashe bai fito a faifan bidiyon ba.

Duk kokarin tabbatar da faruwar lamarin daga hannun rundunar ‘yan sandan jihar Legas PPRO, SP Benjamin Hundeyin, ya ci tura domin bai amsa ba lokacin da SaharaReporters ta kira shi ta wayar salula. Shima bai amsa sakon da aka tura masa ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN