A cewar PDPn, idan tsohon shugaban kasar bai yi karin haske kan kalaman da aka danganta da shi ba cikin awa 48, jam'iyyar za ta fada wa yan Najeriya ainihin ko wanene Obasanjo.
Da ya ke magana a taron manema labarai a Kaduna a ranar Litinin, Shugaban Kwamitin amintattu na PDP, Sanata Walid Jibrin, kuma ya bayyana cewa an kafa kwamiti don ganawa da gwamnan Rivers Nyesom Wike kan batun mataimakin shugaban kasa.
Ya ce jam'iyyar za ta warware matsalolinta.
A cikin sanawar da aka ce tsohon shugaban kasar ne ya fafi game da Atiku da jaridu suka wallafa, shugaban na BoT ya ce shi da PDP na girmama tsohon shugaban kasar.
Amma, cikin gaggawa ya kara da cewa idan za su yi matukar takaici idan har da gaske ne shi ya furta maganganun da aka danganta da shi.
Don haka, ya ce, "Ina son kira ga tsohon Shugaba Obasanjo ya fito fili ya maimaita abin da ya ce. Ko an yi kuskuren rahoto abin da ya fada ne ko kuma hakan ya ke nufi.
"Duk da cewa bai karyata abin da aka rahoto ba, za a iya tsammanin rahoton gaskiya ne, amma idan bai fito fili cikin awa 48 ya bayyana menene gaskiya ba, za ka ji sako daga gare mu kuma ba ni da zabi sai dai in fasa kwai in fada wa duniya ko wanene Obasanjo.
"Babu shakka akwai yiwuwar Obasanjo har yanzu yana fushi da Atiku duk da ya taimake shi amma ya datse masa damar yin tazarce na uku, Alhaji Abubakar Atiku dan takarar shugaban kasar mu ne kuma ina tabbatar maka insha Allahu zai zama shugaban kasa a 2023."
A wani rahoton, jagoran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC daga Arewa, Abdullahi Aliyu Katsina ya ce kuri'an jin ra'ayin al'umma da kungiyar ta yi ya nuna cewa zaben gwamnan Borno, Babagana Zulum ne kadai a matsayin mataimakin Ahmed Bola Tinubu zai tabbatarwa APC samun nasara cikin sauki.
Katsina, yayin taron manema labarai da aka yi a jiya a Minna ya ce duk da cewa mutanen Borno ba su son ya tafi saboda ayyukan alheri da ya ke yi a jihar, yi wa kasa hidima zai fi dacewa, Leadership ta rahoto.