Tinubu ya nisanta kansa daga tikitin Musulmi da Musulmi


Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress(APC) mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da rade-radin cewa yana shirin daukar dan uwansa Musulmi a matsayin abokin takara
.

Tinubu ya yi jawabin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a yayin gangamin APC da aka gudanar a jiya Talata a Ekiti gabannin zaben gwamnan jihar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Sai dai kuma, ya nesanta kansa daga jita-jitan, yana mai cewa wadanda suke yada ta basa bisa tsarin dimokradiyya kuma sun tsorata ne da nasarar da zai samu a babban zaben shugaban kasa mai zuwa.

Da yan jarida suka tambaye shi game da zabinsa na mataimakin shugaban kasa, sai Tinubu ya jadadda cewa tikitin mataimakin shugaban kasa na yankin arewa masu gabas ne kuma ma kiristoci, koda dai ana kan tattaunawa kan wanda za a tsayar.

Ya ce:

“Tikitin mataimakin shugaban kasar na yankin arewa maso gabas ne kuma ma kiristoci, amma ana kan tattaunawa kan wanda za a yanke hukuncin tsayarwa.”

Tinubu ya ba yan Najeriya tabbacin cewa babu kungiya ko wani mutum da zai iya tursasa mataimakin shugaban kasa a kansa. Ya bayyana cewa zai zabi mataimakin shugaban kasa da kansa kuma wanda zai amfani yan Najeriya, jaridar Independent ta rahoto.

Tun farko dai Tinubu ya yi watsi da batun tikitin Musulmi da Musulmi tun ma kafin a zabe shi a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Da yake zantawa da manema labarai a jihar Ekiti, wani mamba na kungiyar kamfen din Tinubu, Comrade Bolaji Tosin ya kuma bayyana cewa hadin kai, zaman lafiya da aiki shine babban abun da gwamnatin Tinubu za ta baiwa fifiko.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN