
Da dumi-dumi: Sojoji sun gano wata mata da Boko Haram suka sace tun 2014
June 15, 2022
Comment
Dakarun runduna ta 26 Task Force Brigade, a ranar Talata, sun gano wata wata Mary Ngoshe, wacce a cewar rundunar sojin Najeriya, tana daya daga cikin ‘yan matan da aka yi garkuwa da su a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke Chibok a shekarar 2014.
Ngoshe, wadda aka same ta da wani yaro da ake kyautata zaton nata ne, sojojin sun tare ta ne a lokacin da suke sintiri a kewayen Ngoshe a jihar Borno.
Hakan na kunshe ne a wani sako da rundunar ya wallafa a shafin Twitter a safiyar Laraba.
Sakon ya ce:
“Dakarun 26 Task Force Brigade da ke sintiri a kewayen Ngoshe a jihar Borno a ranar 14 ga watan Yuni 2022 sun gano wata mata Mary Ngoshe da danta. Ana kyautata zaton tana daya daga cikin ‘yan matan da aka sace daga GGSS Chibok a 2014. Ana ci gaba da bincikarta.”
Karin bayani na nan tafe...
0 Response to "Da dumi-dumi: Sojoji sun gano wata mata da Boko Haram suka sace tun 2014"
Post a Comment
Rubuta ra ayin ka