Siyasar Kebbi: Jerin kujerun takarar siyasa 18 da bangaren Adamu Aliero za su samar a jam'iyar PDP lokacin zaben 2023


Tsohon Gwamnan jihar Kebbi Adamu Aliero ya tayar da kura a siyasar jihar Kebbi bayan ya sami damar nassarar wadatar da jama'ar bangarensa da wasu kujerun siyasa a jam'iyar PDP bayan ya kasa samun irin wannan dama a jam'iyar APC mai mulki a jihar Kebbi.

Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya tattaro cewa jam'iyar PDP a jihar Kebbi ta ba bangaren Adamu Aliero kujerun mukamin Sanata guda uku, kujerun Yan Majalisar tarayya guda hudu, kujerun Yan Majalisar Dokoki na jihar Kebbi guda goma da kuma kujerar mukamin Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi duk bangaren Aliero ne za su samar da yan takara a jam'iyar PDP a zabukan 2023.

Sakataren jam'iyar PDP reshen jihar Kebbi Abubakar Bawa Kalgo ya tabbatar wa kafar labarai na isyaku.com wadannan alkalumma. 

Kazalika isyaku.com ya gano wani shiri na karkashin kasa cewa cikin Yan kwanaki masu zuwa wasu jiga-jigai a fagen siyasar jihar Kebbi za su canja sheka zuwa jam'iyar PDP, lamari da masana harkokin siyasa ke hasashen cewa hakan zai canza fasali, salo da rawar siyasar jihar Kebbi bisa manufa ta canjin yanayi da sauyawar lokaci kan alkiblar siyasar akida ko jari hujja. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN