Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Adamawa ta kama mafarauta uku da wasu kan hadin baki don garkuwa da mutane a kananan hukumomin Girei da Fufore a jihar, Daily Trust ta rahoto.
Mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Sulaan Nguroje, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce wadanda ake zargin:
"Auwal Muhammad mai shekara 28, Isa Umaru dan shekara 40, da Rabiu Mohammed dan shekara 19 an kama su suna addabar kauyukan Pariya Daware da Girei."
Ya kara da cewa yan sandan sun kwato babur guda daya da bindiga pistols wanda aka kera a Najeriya da wasu kayayyaki daga hannun wadanda ake zargin.
"Binciken da aka yi kawo yanzu ya nuna wadanda ake zargin sun ci amanar da aka basu na tsare rayyuka da dukiyoyin al'umma, suke yi wa masu garkuwa safarar abinci da wasu kayayyaki a yankin," in ji sanarwar.