-->
Shekarau ya sami tikitin takarar Sanata na Kano ta tsakiya a jam'iyar NNPP bayan ya fice daga APC

Shekarau ya sami tikitin takarar Sanata na Kano ta tsakiya a jam'iyar NNPP bayan ya fice daga APC


Sanata Ibrahim Shekarau, ya zama dan takarar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na Sanatan Kano ta tsakiya a zaben 2023. Shafin labarai ta intanet na isyaku.com ya wallafa.

Shekarau ya ci zaben takarar kujerar Sanata a Gezawa, Shelkwatar karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano.

Dr Abdullahi Baffa ya ci zaben tikitin NNPP na Kano ta arewa, yayin da Mr Kawu Sumaila ya sami tikitin Kano ta kudu a zaben da aka gudanar. 

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel