Type Here to Get Search Results !

Wani dan arewa ya kashe dan arewa da duka yayin da suke fada a kudu, duba abin da ya biyo baya


Wata Kotun Majistare a garin Iyaganku ta tasa keyar wani matashi dan shekara 22 mai suna Muhammed Umar zuwa Kurkukun Agodi bayan ya lakaɗa wa wani saurayi dukar tsiya har lahira yayin da suke fada.

Yan sanda ne suka gurfanar da Umar a gaban Alkalin Kotu Mrs Patricia Adetuyibi bisa tuhumar kisan kai.

Mai gabatar da kara na Yan sanda Insp Salewa Hammed ya gaya wa Kotu cewa wanda ake tuhuma ya kashe wani matashi mai suna Dan Mallam Mai shekara 23 a Duniya da karfe 2:30 na dare yayin da suke fada ranar 6 ga watan Mayu.

Umar bai amsa laifinsa ba a gaban Kotu, sakamakon haka Kotu ta yi umarnin a kai shi Kurkuku har ranar 15 ga watan Agusta domin ci gaba da sauraron shari'ar. Tare da bayar da dama na tuntubar ofishin DPP na jihar kan shari'ar.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies