Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun shiga Abuja da sanyin safiya, sun sace mutane da dama


Wasu tsageru da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a safiyar ranar Litinin sun kai hari a jerangiyar gidaje na Gwarinpa da ke babban birnin tarayya.

Daily Trust ta gano cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki a gidajen ne tsakanin karfe 1 na dare zuwa karfe 4 na asuba, inda suka yi awon gaba da wasu mutanen da har yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Ko da yake har yanzu babu cikakken bayani, wani mazaunin garin, wanda kawai ya bayyana sunansa da Mohammed ya ce ‘yan bindigar sun samu shiga jerangiyar gidajen Genuine katin shiga na Efab Queens da ke 6th Avenue, Gwarinpa.

Ya bayyana wa majiya ta wayar tarho cewa ’yan bindigar na dauke da baka, da kibiyoyi, da adduna kuma suna da yawa.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta shaida cewa lamarin fashi ne ba na garkuwa da mutane ba.

Adeh, mataimakiyar Sufeton ‘yan sanda, ta ce tuni aka tattara ‘yan sanda zuwa wurin domin sanin yadda lamarin ya faru da nemo mafita.

Ta yi alkawarin cewa za a sanar da jama'a abin da ya kamata bayan an gano cikakkun bayanai kan lamarin.

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE