Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta gurfanar da wasu mutane hudu da ake zargi da laifin kona wani mutum mai shekaru 57 har lahira bisa zargin maita.

 


Rundunar ‘yan sanda a jihar Adamawa ta kama wasu masu matsakaitan shekaru hudu bisa laifin kashewa da kona wani magidanci mai suna Benson Timothy dan shekaru 57, wanda suka zarga da maita a karamar hukumar Guyuk ta jihar Adamawa a ranar 15 ga Mayu, 2022.

A cewar rundunar ‘yan sandan, masu matsakaicin shekaru masu suna Ezekiel Kumtha, Awo Mesa, Ishaku Sanda, da Oga Dapila, sun zargin marigayin da aikata maita tare da haddasa mutuwar yara kanana a cikin al’umma.

Mutanen dai sun dora laifin ne a kan wanda aka kashen a wurin shan ruwa sannan suka jefe shi da kulake tare da jifansa da duwatsu kafin suka banka masa wuta.

A cikin takardun kotun da aka shigar kan wadanda ake zargin a gaban wata kotun majistare da ke jihar, dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Zakka Musa ya yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun hada baki ne da aikata laifuka tare da kai wa marigayin, Benson Timothy, hari a ranar.

A cewar masu gabatar da kara, laifukan da suka hada da hadin baki da kuma kisan kai, sun ci karo da sashe na 60 da 192 na dokar Penal Code na shekarar 2018.

Bayan wadanda aka gurfanar a gaban Kotun sun musanta aikata laifi kan kan tuhume-tuhume guda 2 da aka yi masu, Alkalin ya ba da umarnin a tsare su a gidan yari tare da dage karar zuwa ranar 5 ga Yuli, 2022.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN