Da dumi-dumi: Kotu ta umarci a kwace jami'a da otal a Kaduna na babban jami'in gwamnati

 


Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Laraba, 1 ga watan Yuni, ta bayar da umarnin kwace duk wasu kadarorin jami’ar NOK da ke Kaduna na wucin gadi.

A cewar wata sanarwa da hukumar EFCC ta fitar, jami’ar da tsohon Daraktan kudi da asusu (DFA) na ma’aikatar lafiya ta tarayya Anthony Hassan ya gina, ana zargin an gina ta ne daga kudaden haramun da aka gano daga mai ita.

Hassan, wanda DFA ne a ma’aikatar tsakanin 2016 zuwa 2019 ana zargin ya gina Jami’ar ne da kudin almundahana.

“Kadarori na Jami’ar da aka kwace sun hada da ginin majalisarta, ginin ICT, rukunin gine-ginen likitanci, ginin sashen Kimiyya, gine-ginen Ilimi guda biyu, dakin karatu da sauran gine-gine.

“Sauran kadarorin da aka gano da ke da alaka da Hassan wadanda kuma aka kwace su na wucin gadi sun hada da Gwasmyen Water Factory, Gwasmyen Event Center da Gwasmyen International Hotel da ke Kaduna.”

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Mai shari’a Zainab Abubakar, ta bayar da umarnin kwace kadarorin ne na wucin gadi yayin da take yanke hukunci kan wani kudiri da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gabatar.

Lauyan EFCC, Ekele Iheanacho ya shaida wa kotun cewa EFCC ta nemi wannan umarni ne bisa ga sashe na 44 (2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 kuma sashe na 17 na kudin zamba da sauran laifukan da suka danganci doka ta 14, 2006 da kuma ikon kotu.

A hukuncin da kotun ta yanke, kotun ta bayar da umarnin a buga wannan doka na wucin gadi a cikin jaridun kasar nan, inda ta sanar da duk mai ta cewa kan kadarorin da ya bayyana, a cikin kwanaki 14, domin kalubalantar lamarin

Mai shari’a Zainab Abubakar ta dage sauraron karar har zuwa ranar 5 ga Oktoba, 2022, domin sake duba lamarin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN