Da dumi-dumi: Yan ta'addar Ansaru sun kai hari kan masu ababen hawa, sun kona motoci 8, sun yi awon gaba da fasinjoji da dama a Birnin-Gwari


Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar ta’addar Ansaru ne a ranar Talata sun kai hari kan masu ababen hawa a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, inda suka yi awon gaba da fasinjoji da dama a yayin samamen. Daily Nigerian ta ruwaito
.

Da yake aiko da sautin muryar SOS, wani mazaunin Birnin Gwari da ya tsallake rijiya da baya, Haruna Abubakar, ya ce ‘yan ta’addan sun kuma kona motoci kusan takwas, ciki har da wata mota makil da kayan abinci.

Mista Abubakar wanda ya yi ikirarin cewa ma’aikacin KASTLEA ne ya kara da cewa ‘yan ta’addan sun shafe sama da mako guda suna gudanar da ayyukansu a kan hanyar ba tare da daukar matakan tsaro ba.

Yayin da yake kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kawo musu dauki, Mista Abubakar ya ji tsoron cewa idan ba a yi wani abu ba, garin Birnin-Gwari zai zama matsugunin ‘yan ta’addan.

Da take tabbatar da faruwar harin, kungiyar tsaro ta Birnin-Gwari Vanguards for Security and Good Governance a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata ta ce lamarin ya faru ne tsakanin Kuriga da Manini kusa da Udawa.

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugabanta Ibrahim Abubakar-Nagwari, ta shawarci masu ababen hawa da su daina bin hanyar har sai an daidaita matsalar tsaro.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN