Rahotannin sirri: Sanatoci 20 na shirin ficewa daga APC, mafi rinjayen jam'iyyar na fuskantar barazana a Majalisar Dattawa


Sabbin rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na iya rasa rinjaye a Majalisar dattawa.

Hakan ya biyo bayan rahoton da ke cewa akalla Sanatocin APC 20 ne suka kammala shirin ficewa daga jam’iyyar.

Legit.ng ta ruwaito cewa rahotanni sun bayyana cewa Sanatocin na sa ido a kan jam’iyyun PDP, Labour Party, New Nigeria Peoples Party da sauran su.

Ku tuna cewa a baya jam’iyya mai mulki ta rasa ‘yan Majalisar Dattawa 13 a jam’iyyun adawa.

‘Yan Majalisar dai sun fusata ne bayan sun rasa tikitin komawa Majalisar Dokokin kasar a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

A halin yanzu, kananan jam’iyyu biyar da ke babban zauren Majalisar na da Sanatoci 43 yayin da PDP ke alfahari da Sanatoci 39, yayin da Jam’iyyar Young Peoples Party, All Progressive Grand Alliance, Labour Party da New Nigeria People’s Party ke da Sanatoci hudu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, dan Majalisar da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa dole ne shugaban jam’iyyar ya sauka a Majalisar Dokokin kasar domin hana Sanatocin ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki.

An ruwaito dan Majalisar yana cewa:

“Shugaban jam’iyyar ya zo ganawa da Sanatocin APC ne saboda ya ce ta hanyar leken asiri sun samu cewa wasu Sanatoci akalla 20 na shirin sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu nan da mako guda.

“Shugaban ya bukaci kowanne Sanatocin da suka koka da su bayyana kokensu wanda muka yi daya bayan daya. Da ya ji matsalolinmu, sai shugaban jam'iyar  ya ba da umarnin mu rubuta su a rubuce.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN