Kuma dai: Yan bindiga sun yi awon gaba da DPO a Nasarawa, sun bukaci a biya su N5m, duba yadda ta faru


Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da jami’in ‘yan sanda (DPO) a karamar hukumar Nasarawa Eggon a jihar Nasarawa, CSP Haruna Adulmalik. Kafar labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

An yi garkuwa da DPO mai kula da sashen Nasarawa Eggon, da misalin karfe 9:30 na daren Laraba, 22 ga watan Yuni, a kan hanyar Bakyano zuwa Arikya yayin da ya dawo daga sa idon jami’an da aka tura domin samar da tsaro a hanyar.

An tattaro cewa DPO din ya ci karo da masu garkuwa da mutane inda suka yi wa hilux da ke sintiri kwanton bauna suka tafi da shi. 

Kwanakin baya DPO ya gudanar da taron tsaro a yankin tare da duk masu ruwa da tsaki inda ya bayyana aniyarsa na ganin manoma da makiyaya sun sami girbi mai yawa a wannan kakar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan DPO inda suka bukaci a biya su N5m domin a sake shi. 

Mai kula da ci gaban yankin Akun na karamar hukumar Nasarawa Eggon, Honarabul Moses Anvah, wanda ya tabbatar da sace DPO, ya ce sun kai kara ga kwamishinan ‘yan sanda.

Mataimakin shugaban karamar hukumar Nasarawa Eggon, Engr Benjamin Kuze, ya shaidawa jaridar The Nation cewa DPO din na dawowa ne daga wani sintiri a kusa da hanyar Bakeno/Arikya a lokacin da ya ci karo da masu garkuwa da mutanen.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN