Masu garkuwa da mutane sun kashe tare da binne jami’in Polytechnic na Zamfara bayan sun karbi kudin fansa na N4m daga iyalansa


Wasu masu sace mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe tare da binne wani jami’in kula da harkokin dalibai a makarantar Abdu Gusau Polytechnic Talata-Mafara, jihar Zamfara, Sanusi Haliru, bayan sun karbi kudin fansa na N4m daga iyalansa.

An dai yi garkuwa da Haliru ne a hanyar Abuja zuwa Kaduna a kan hanyarsa ta zuwa halartar wani taron karawa juna sani kafin yi wa kasa hidima a Abuja. Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalansa inda suka bukaci a biya su N4m domin a sake shi, amma ba a samu kudin ba a lokacin.

Wani dan uwan ​​mamacin mai suna Mohammed Nasir wanda ya zanta da Punch ya ce bayan sun tara N4m, dangin sun kira ‘yan fashin inda suka tambaye su inda za su biya kudin fansa.

“Shugabansu ya ba mu wani wuri kuma ya gaya mana cewa wani zai zo ya karbi kudin. Da muka isa wurin, ba mu ga kowa ba. Nan take sai muka ga wasu sun nufo wajenmu a kan babur, nan take suka iso, suka ce mu samar da kudin. Muka mika musu kudin sai daya daga cikinsu ya shaida mana cewa dan uwanmu ya rasu

Mun nemi gawar ne domin mu shirya Sallar jana’izarsa, amma abin takaici sai suka ce mana ya rasu ne tuntuni kuma an binne gawarsa. Sai suka koma maboyarsu suka bar mu cikin wani hali mai tsanani.” Inji Nasir

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN