NNPP da Labour Party waye zai zama mataimaki tsakanin Kwankwaso da Peter Obi, an fitar da bayani


Biyo bayan tambayar ko wanene zai dora wa daya hannu tsakanin Rabiu Kwankwaso da Peter Obi idan har an samu hadewar jam’iyyar New Nigerians Peoples Party (NNPP) da Labour Party, wani jigo ya yi bayani. 

Sakataren yada labaran jam’iyyar NNPP na kasa, Agbo Major, ya ce ana ci gaba da tattaunawa kan kawancen jam’iyyun biyu ba tare da wata matsala ba. 

Daily Trust ta rahoto cewa Major ya tabbatar da cewa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan majalisa a majalisar dokokin kasar na iya amincewa da zama abokin takarar Obi wanda shine dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour. 

Major ya kara da cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin manyan bangarorin biyu da mutane da dama suka bayyana a matsayin karfi na uku da zai iya ceto Najeriya,. 

Kalamansa: "

A lokacin da muka gama tattaunawa, 'yan Najeriya za su yi farin ciki, ko wacce hanya ta kasance." 

Jam’iyyar Labour ta bayyana Doyin Okupe, wanda tsohon babban mai taimaka wa Goodluck Ebele Jonathan ne, abokin takarar Peter Obi. 

An aika sunan Okupe ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni, ga INEC , domin ta doke wa’adin mika sunayen ‘yan takara. 

Sai dai majiyoyin yada labarai sun bayyana cewa Okupe ya kasance wanda zai tsaya takarar dan takara na hakika wanda za a bayyana shi kafin zaben 2023. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN