
Kwana biyu bayan shafe shekara biyu a Kurkuku saurayi dan shekara 17 ya sake tafka sata ya dambace makwabta da suka kama shi (Bidiyo)
June 19, 2022
Comment
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta sake kama wani matashi dan shekara 17 da aka sako daga gidan yari kwanaki biyu da suka gabata bisa laifin shiga gidan wani.
Da yake wallafa bidiyon wanda ake zargin a shafin Twitter, kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya rubuta;
“An sako wannan matashi mai shekaru 17 daga gidan yari kwanaki biyu da suka wuce bayan ya yi shekaru biyu don kasancewa dan kungiyar asiri. Jiya ya shiga gidan wani ya kwashe kaya masu daraja. Menene ainihin kuskurenmu? NB: Lebbansa...ya yi taho-mu-gama da makwabta da suka kama shi, ba ‘yan sanda ba.
Kalli bidiyon wanda ake zargi da aikata laifin a kasa....
0 Response to "Kwana biyu bayan shafe shekara biyu a Kurkuku saurayi dan shekara 17 ya sake tafka sata ya dambace makwabta da suka kama shi (Bidiyo)"
Post a Comment
Rubuta ra ayin ka